Hon Alhassan Ado Doguwa YA BADA NAIRA DUBU DARI 2 GA DALIBAN MAKARANTAR AHBABU RASULILLAH SU 40 DA SUKA YI SAUKAR KARATUN ALKUR, ANI MAIGIRMA
Shugaban Yan majalisun Arewacin Nijeriya Rt Hon Alhassan Ado Doguwa sardaunan kasar hausa Mai tuta (OON) yaja hankalin matasa da su kasance masu neman Ilimi kowanne.Domin tafiya da zamani yadda ya kamata
Alhassan Ado yayi wannan kiranne Alokacin da ya halarci taron bikin saukar karatun Alkur, Ani maigirma na makarantar Ahbabu RASULILLAH dake Garin ruwan tabo a yankin karamar hukumar Tudun wada.
Mai magana da yawun Hon Alhassan Ado Doguwa, Auwal Ali Sufi utai ne ya wallafa wannan bayanin a shafinsa na kafar sadarwa ta fecebook.
Dadin dadawa Hon Alhassan Ado Doguwa ya bada Tallafin kudi kimanin naira dubu Dari biyu ga Daliban da suka sauke karatun Alkur, Ani maigirma su 40 na makarantar..
Hon Alhassan Ado ya hori Daliban da su ji tsoron Allah suyi Amfani da abinda suka koya domin samun rabo duniya da Lahira.
