JAM, IYYAR APC :YAKAMATA KOWANNE DAN JAM, IYYAR APC YAJE YAYI KATIN SHAIDAR JAM, IYYA DAN CIGABA DA RABA ROMON DIMUKRADIYYA A YANKIN KANANAN HUKUMOMIN TUDUN WADA DA DOGUWA
Dukda kasancewar, yankin kananan hukumomin tudun wada da Doguwa, yankine da jam, iyyar Apc take rabawa yayan ta romon Dimukradiyya, shugaban Yan majalisun Arewacin Nijeriya Rt Hon Alhassan Ado Doguwa yasha Alwashin cigaba da bada tallafin kudade ga mata, Maza da matasa domin yin Jari domin Dogaro dakai.
Hon Alhassan Ado yayi Dogon bayani ga Matasan yankin dangane da mahimmancin yin kuri, ar jam, iyyar Apc.
Hon DOGUWA yayi bayani Mai tsawo bisa mahimman cin Katin jam, iyyar ta Apc.
Haka zalika ya sake Jan hankalin matasa da mata da su tabbatar sun yi Katin zabe da hukumar zabe take gudanar wa a yanzu haka.
Wannan bayanin na kunshe a shafin Mai magana da yawun Rt Hon Alhassan Ado Doguwa, Auwal Ali Sufi utai. ya bayyana cewar Hon Alhassan Ado na cigaba da nuna goyan baya ga shigowar Gwamnan Jihar kano cikin jam’iyyar APC, kana ya yi kira ga yayan jam, iyyar Apc na yankin kananan hukumomin tudun wada da Doguwa da su cigaba da bada hadin Kai da goyan baya domin nasarar jam, iyyar Apc a kowanne mataki.
