Shugaban majalisar dokokin jihar Borno ya nuna fushinsa kan rashin sanya hoton Shettima a taron APC
Kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Abdulkarim Lawan, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan cire hoton mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, daga cikin hotunan shugabannin jam’iyyar APC da aka nuna a wata bana na taron jam’iyyar a yankin.
Bana ɗin ta ƙunshi hoton shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnonin APC guda biyar na Arewa maso Gabas, da mai ba jam’iyya Shawara kan shari’a na ƙasa , amma ba a saka hoton mataimakin shugaban ƙasa ba.
A yayin da yake bayyana ra’ayinsa, kakakin majalisar ya ce bai dace ba a gudanar da taron ba tare da hoton Shettima ba, musamman ma a garinsa na haihuwa.
Ya kuma tuna da cewa irin wannan cire hoto ko suna ne ya janyo rikici a taron APC na Jihar Gombe a bara.
Korafin kakakin majalisar ya samu goyon bayan jama’a da suka hallara, inda suka nuna rashin amincewa da wannan mataki.
A halin yanzu, gwamnonin APC da sauran masu ruwa da tsaki suna Maiduguri domin halartar zaman sauraron ra’ayin jama’a na shiyyar Arewa maso Gabas kan gyaran kundin tsarin jam’iyyar APC.
