Kungiyar Ƙwadago ta kasa NLC data ma’aikata TUC zasu gudanar da maci a gobe a titunan Abuja domin nuna goyon baya ga ma’aikan burnin dake kukan rashin albashi.
Ƙungiyoyin sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da Babban Sakataren NLC, Mista Benson Upah, da Babban Sakataren TUC, Nuhu Toro, suka sanya wa hannu.
Wannan goyon bayan na zuwa ne domin tallafa wa yajin aikin da ma’aikatan Hukumar Ci Gaban Babban Birnin Tarayya FCDA, suka shiga sakamakon rashin biyan albashinsu.
Ma’aikatan da ke ƙarƙashin kungiyar JUAC sun fara yajin aikin sai baba ta gani ne a ranar 19 ga Janairu, lamarin da ya haifar da rufe muhimman ofisoshin gudanarwa, ciki har da Sakatariyar Hukumar Babban Birnin Tarayyar FCDA.
