Shugaban Yan majalisun Arewacin Nijeriya Rt Hon Alhassan Ado Doguwa sardaunan kasar hausa Mai tuta (OON) ya jajantawa Yan kasuwar singa bisa Iftila’in gobara da ya sake afka musu.
Hon Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewar Allah madaukakin sarki yana iya jarabtar bayinsa da Abubuwa kala – kala, Muddin dai ka yi Imani.
Cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun Rt Hon Alhassan Ado Doguwa ya fitar Auwal Ali Sufi utai a shafinsa na kafar sadarwa.
Your message has been sent
Hon Alhassan Ado Doguwa yayi Addu, ar Allah ya mayar musu da Alheri Allah ya kiyaye afkuwar hakan nan gaba.
Hon Alhassan Ado ya Taya Al, ummar musulmi murnar shigowar watan Azumin Ramadan tare da yin kira ga masu hannu da shuni da su tallafawa Mata da tsofaffin da marayu domin samun Babban rabo a ranar Alkiyama.
Doguwa ya yiwa AL, ummar musulmi fatan Allah ya sa a kammala Azumin Ramadan lafiya tare da fatan Alheri
