Gwamnatin Jigawa Ta Ba da Kwangilar Gyaran Sakatariyar Masarautar Gumel
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ba da kwangilar gyaran ginin Sakatariyar Majalisar Masarautar Gumel, a wani mataki na inganta gine-ginen cibiyoyin masarautu da ƙarfafa ayyukansu.
Daraktan Harkokin Sarauta da ke Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Alhaji Babandi Habu, ne ya bayyana hakan yayin da yake miƙa wurin aikin ga wakilin kamfanin Alhumaidi Global Impex Limited domin fara aikin.
Ya ce ana sa ran kamfanin zai kammala aikin gyaran cikin makonni goma sha biyu (12), yana mai bayyana cewa aikin wani muhimmin jari ne da gwamnatin jihar ta zuba domin inganta gine-gine da ayyukan Majalisar Masarautar Gumel.
Alhaji Babandi Habu ya jaddada cewa gwamnatin Jigawa na ci gaba da jajircewa wajen samar da ingantaccen aiki a hukumomin gwamnati tare da ƙara wa cibiyoyin gargajiya ƙarfi domin su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
A nasa jawabin, wakilin kamfanin Alhumaidi Global Impex Limited, Alhaji Sanusi Ahmed Adamu, ya tabbatar da cewa kamfanin zai gudanar da aikin cikin inganci tare da bin duk sharuɗɗan da ke cikin kwangilar da aka kulla.
— Ƙarshe —
Related Posts
Add A Comment
