Kamar yadda wata sanarwa da ta fito daga ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Jigawa wadda Jami, in hulda da jama a na ofishin kwamaredisma, I’ll Ibrahim Dutse ya rattabawa hannu.
Gwamnan Jihar Jigawa State, Malam Umar A. Namadi, ya amince da dakatar da wasu mataimakansa guda huɗu daga aiki ba tare da ƙayyadadden lokaci ba.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Bala Ibrahim, ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta bayyana sunayen waɗanda abin ya shafa kamar haka:
Abbas Makama – Babban Mataimaki na Musamman kan Kula da Ambaliya.
Salisu Muhammad (Rosy Auyo) – Mataimaki na Musamman kan Harkokin Kasuwanci da Sana’o’i.
Ibrahim Yunusa – Mataimaki na Musamman kan Saka Ido a Fannin Ilimin Firamare.
Umar Abdulkadir (Alhaji Bullet Auyo) – Mataimaki na Musamman kan Noman Ƙungiyoyi (Cluster Farming).
Sanarwar ta ce dakatarwar ta fara aiki nan take, ba tare da wani jinkiri ba.
An fitar da sanarwar ne ta hannun Isma’ila Ibrahim Dutse, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, a ranar 1 ga Yuni, 2026.
