Allah Ya Yiwa Sardaunan Sokoto Alhaji Abubakar Alhaji (Alhaji Alhaji) Rasuwa
Tsohon jakadan Najeriya a Birtaniya kuma Sardaunan Sakoto, Alhaji Abubakar Alhaji, ya rasu yana da shekaru 94 a duniya.
Ya rasu ne da safiyar Alhamis a Asibitin Alliance da ke Abuja bayan shafe makonni yana jinya, inda aka mayar da shi daga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo (UDUTH) da ke Sakoto kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Dikkon Sokoto, Alhaji Ya’u Dogon Daji, ya tabbatar da rasuwarsa, yana mai cewa marigayin ya yi fama da rashin lafiya kusan wata guda, kuma ana sa ran za a yi masa sallar jana’iza a Masallacin Sultan Bello da ke Sakkwato kafin a binne shi a Hubbaren Shehu.
Marigayin ya fara aikin gwamnati a 1964, inda ya rike mukaman Babban Sakatare a Ma’aikatun Kasuwanci da Kudi, sannan ya zama Karamin Ministan Kasafi da Tsare-tsare a gwamnatin Janar Ibrahim Babangida kafin daga bisani ya zama Ministan Kudi tsakanin 1990 zuwa 1991. Haka kuma ya taba zama Babban Kwamishinan Najeriya a Birtaniya.
Ya bar mata, ‘ya’ya biyar, jikoki da sauran ‘yan uwa, ciki har da tsohuwar Karamar Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Hajiya Aisha Abubakar.
