Shugaban Yan majalisun Arewacin Nijeriya Rt Hon Alhassan Ado Doguwa sardaunan kasar hausa Mai tuta (OON) ya raba kabakin Arziki a yankin karamar hukumar Tudun wada.

RT Hon Alhassan Ado ya bayyana cewar a kowanne lokaci, jam, iyyar Apc na maraba da kowa, domin cigaban yankin karamar hukumar Tudun wada.
Tun da farko a jawabin sa Danmajalisar jiha Mai wakiltar karamar hukumar Tudun wada a majalisar Jiha Hon sule Lawan shuwaki ya bayyana cewar Rt Hon Alhassan Ado Doguwa ya bada Tallafin kudi da kayan Abinci ga yayan jam, iyyar Apc na karamar hukumar Tudun wada, yayin da ya Kara da cewar kungiyoyin matasa da Mata zasu Amfana musanman ma kasancewar zuwan watan Azumin Ramadan.

Yayinda a gefe guda shugaban jam, iyyar Apc na karamar hukumar Tudun wada Hon suyudi Umar full game ya bayyana cewar jam, iyyar Apc a karamar hukumar Tudun wada guda daya ce karkashin jagorancin shugaban Yan majalisun Arewacin Nijeriya Rt Hon Alhassan Ado Doguwa sardaunan kasar hausa Mai tuta.
Tuni dai kungiyoyin matasa da Mata suka karbi tallafin su da sauran mazabu,.
