Gwamna Yusuf da Wasu Gwamnoni Sun Yaba wa Sheikh Jingir, JIBWIS Ta Goyi Bayan Tinubu/Shettima a 2027
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da takwarorinsa na jihohin Yobe, Sakkwato da Jigawa, sun yaba wa Shugaban Majalisar Malamai ta ƙasa na ƙungiyar Jama’atul Izalatul Bid’a Wa Iqamatussunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, bisa ƙoƙarinsa na ci gaba wajen inganta haɗin kai, zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin Musulmi da sauran al’ummar Nijeriya.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Lahadi.
Gwamnonin sun bayyana yabon nasu ne a yayin wani taron tattaunawa na ƙasa na yini guda mai taken: “Ƙara Ƙarfafa Shiga Harkokin Siyasa da Tallafa wa Adalci a Matsayin Hanyar Samar da Haɗin Kai da Ci Gaba a Nijeriya”, wanda aka gudanar a Saddiqa Event Centre da ke birnin Jos, jihar Plateau.
Taron ya kuma shaida wani babban ci gaba na siyasa, inda ƙungiyar JIBWIS ta yi kira ga mambobinta a faɗin ƙasar nan da su goyi bayan tare da zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima, a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban JIBWIS na ɓangaren gudanarwa, Sheikh Abdulnasir Abdulmuhuyi, ya bayyana cikakken amincewarsa da gwamnatin Tinubu da Shettima, yana mai cewa Gwamnatin Tarayya ta nuna amana da jajircewa wajen ci gaban Nijeriya a cikin shekaru uku na farkon wa’adinta.
Sheikh Abdulmuhuyi ya ce gwamnatin ta cancanci samun goyon bayan ‘yan Nijeriya domin ta sake samun wa’adi na biyu, domin ci gaba da ƙarfafa nasarorin da ta samu tare da aiwatar da manufofinta na ci gaban ƙasa.
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Malamai ta JIBWIS na ƙasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya buƙaci mambobin ƙungiyar a duk faɗin Nijeriya da su sabunta goyon bayansu ga Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima gabanin zaɓen 2027.
Da yake magana a madadin gwamnonin jihohin Kano, Sakkwato, Jigawa da Yobe, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya tunatar da tarihin siyasar Nijeriya, musamman zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 1993, lokacin da Marigayi Chief MKO Abiola ya tsaya takarar shugaban ƙasa tare da Musulmi a matsayin mataimakinsa, Ambasada Babagana Kingibe.
Gwamna Buni ya yaba wa Sheikh Jingir bisa jajircewarsa da ƙudirin da yake nunawa wajen inganta haɗin kan ƙasa ta hanyar wa’azinsa, yana mai cewa irin waɗannan ƙoƙari na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa zaman lafiya tsakanin ‘yan Nijeriya.
A nasa saƙon fatan alheri, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya ba za su iya rasa gwamnatin Tinubu da Shettima a shekarar 2027 ba.
Sanata Barau ya kuma yaba wa Sheikh Jingir bisa gagarumin ƙoƙarinsa na inganta haɗin kai da zaman lafiya a faɗin ƙasar nan.
A wani ɓangare kuma, Hon. Ibrahim Kabir Masari da Gwamna Mai Mala Buni sun bayar da gudummawar Naira miliyan 300 kowannensu domin kafa Jami’ar Fortune University, wadda Sheikh Sani Yahaya Jingir ya assasa.
Taron ya haɗa fitattun malaman addinin Musulunci, jagororin siyasa, jami’an gwamnati da mambobin JIBWIS daga sassa daban-daban na ƙasar nan, inda suka tattauna kan shiga harkokin siyasa, adalci, haɗin kan ƙasa da ci gaba mai ɗorewa a Nijeriya.
Related Posts
Add A Comment
