Yau rana ce mai cike da tarihi a Najeriya!
A rana irin ta yau a 1966 ne aka kashe Firaiministan Najeriya na farko, Tafawa Ɓalewa da Firimiyan Arewa, Ahmadu Bello da wasu jiga-jigan ƴansiyasa da sojoji a yunƙurin sojoji na juyin mulki.
Ahmadu Bello ne firimiyan jihar Arewa na farko a tarihi kuma akwai wasu sanannun mutane da suka riƙe muƙamin minista a ƙarƙashinsa.
Wane Irin Kisa Akayiwa Sir Ahmadu Bello Sardauna? Yau Shekaru 60 Kenan!!
Kisan da akaima Sardauna a gidan Gwamnatin Jahar Arewa dake Kaduna. Da yawan mutane sunyi maganganu, wasu maganganunma ba su da kangado, babu ilimi ko daya a ciki. Dayawan labaran da mutane suke yadawa hankali bazai dauka ba.
Hakan yasa na zurfafa bincike sosai dan mu gane shin wane irin kisa akayiwa Sardauna? Wasu mawakan hausa da wasu mutane makusantar Sardauna, sun bada wasu labarai wayanda hankali ba zai dauke su ba.
Bincike ya tabbatar da cewa shi wanda ya jagoranci, kisan su Sardauna Manjo Patrick Chukuma Kaduna Nzeogwu, ya dade da kullantar Sardaunan a ransa, hakan ya sa ya fara horar da wasu sojoji wanda mafi yawancinsu yan Arewa ne.
NZEOGWU YA KADDAMAR DA SAMAME MASU SUNA KAMAR HAKA. OPERATION.
Ya kaddamar da Samame masu Sunaye Kamar Haka
Damisa
Zaki
Giwa
Irin wannan samamen shi Nzeogwu ya yi ta ba wa sojojin horo a kai. Sukan kansu sojonin basu san dalilin da yasa yake basu wannan horon ba. Kullun dare yakan tarasu suyi tayin wannan Atisayen har Asuba. Duk da cewa manyan sojoji na kallonsa sukansu basu da masaniyar dalilin da yasa yake basu wannan horon ba, ya fake da cewar ya kamata ace sojoji na cikin shiri, kuma su rika jiran ko ta kwana.
Ranar 15 ga watan Janairun 1966, juma’a wurin karfe goma Sha biyu na dare, Nzeogwu ya kwaso wasu kuratan sojoji su 45, wasu ma sukace su 50, yan Arewacin Najeriya. Nzeogwu, ya kai su wani wuri inda a yanzu wata makarantar aikin noma take a Mando. A wancan lokacin wurin kungurmin dajine. Daga nan ne suka taso suka nufo Gidan Sardauna. Bincike ya tabbatar da cewar ya kashe wani soja daya da ya nemi yai masa taurin Kai. Kamar yadda abun ya faru wannan sojan ya tsananta da tambayar cewa wane irin aiki na musamnan za suyi? A inane kuma za suyi wannan aikin na musamman? Kuma yaya yanayin aikin yake?
Bayan isowarsu kofar gidan Sardauna, Nzeogwu, ya nunawa wayannan sojojin daya kwaso cewar kunsan ko nan gidan waye? Suka amsa masa da cewar gidan baban duk wani dan Arewa ne Sardauna. Nzeogwu yace musu to mai Gidannan shi muka fito kashewa. Nan take wani Sagent Bayaraben Ilori, Sagen Duru, yace Allah ya kiyaye shi, ya sa hannu a kashe Babansa. Bincike ya tabbatar da cewa Sagen Duru yayi yunkurin tsalake titi ya gudu, amma nan take Nzeogwu, ya harbeshi.
Makaman da Nzeogwu yazo dasu gidan Sardauna sun fi karfin na juyin mulki sai dai na yaki da wata kasa. Nan take Nzeogwu ya umarci wani kurtun soja dan asalin Jahar Kebbi Musa Manga, yace ya harba bindigar da ake amfani da ita wurin kakkabo jirgin saman yaki MM 400× a saman rufin nakin da Sardauna yake.
Karar wannan bindigar ta tada hankalin duk wani mutumin dake Unguwar shanu, da Unguwar sarki. Wannan bindigar itace tasa rufin dakin ya Kamada wuta. Sardauna da matansa da yaran da yake rike da su na yan’,uwa da abokan arziki da duk ma’aikatan dake gidan sun taru a farfadiyar da ake wajen fakin din mota na gidan.
Sardauna ya tsinci kan sa a wani hali na ba shi da wani mataimaki sai na Allah. Ba shi da makamin da zai kare kansa ballema ya kare iyalansa dashi. Bincike ya tabbatar da cewar anan farfajiyar ajiye motocin ne Nzeogwu ya samu Sardarna da matansa guda uku da Larai matar Ali Odilin Sardauna, da Ali Odilin.
Anan an samu mabambamtan maganannu, matan Sardauna Jabbo da Goggon Bichi sun bada labari iri daya, duk da cewar ba lokaci daya akayi hirar da su ba.
JABBO.
Tace duk kan mu muna cikin fargaba mun rude saboda matsanancin karar harbe harbe da mu ke ji a wannan lokacin. Sardauna na tsaye ne yana jan carbi, Hafsat uwargidansa ta na rungume da shi dukkanmu muna kuka mun rasa inda zamu saka kan mu. Da abubuwa sukayi tsanani shi Sardauna yace mana ni tawa ta ka re ku nake ma addu’ar Allah ya kare ku daga sharin waɗannan mutanan. Hafsat ta rike Sardauna da karfin tsiya nima ina manne da jinkinsa haka Goggon Bichi, Larai matar Ali Odali na kusa dani.
Lokacin da Nzeogwu ya zo, ya zo ne da wata fitila mai haske irinta ta mafarauta a goshinsa da yake gidan akwai duhu babu wuta da farin hankici a wuyansa. Da yake muna da yawa da yara damu matanshi mun kewayashi a wannan lokacin.
Nzeogwu ya yi ta mana barazanar cewa idan bamu kauce ba zai harbemu ya kashe mu dukkan mu. Amma mukayi burus da shi. Bayan kokarin sa mana karfi da yayi mu kayi masa turjiya, yasa kan bindiga ya buge ni a goshi, jini na yai tsartuwa na fadi sumammiya. Tace kamar yadda abubuwa suka faru a nan ne dai Nzeogwu ya harbi Sardauna a goshi da zuciyarsa
GOGGON BICHI.
Tace lokacin da Nzeogwu yazo da fitila mai haske a goshin sa da farin hankici a wuyansa. Mu kuma dukkanmu mun kewaye Sardauna, Hafsat ta rike shi kam-kam. Jabbo ma na rike da shi nima ina manne da shi. Nzegowu yayi barazanar zai harbe mu, amma mu da yara kuka kawai muke muna salati. Goggon Bichi tace tana da yakinin cewa kafimma shi Nzeogwu ya harbi Sardauna Allah ya zare ran Sardaunan. Ta kawo dalilai kwarara guda biyu da yake tabbatar da abun da ta ke fada.
Abu na farko tace babu yadda za a sa kan bindiga a bugi daya daga cikin matansa har ta fadi ta suma, ace Sardaunan bai yi magana, ba tace abu ne wanda ba mai yiwuba.
Goggon Bichi, ta ce Koda mai zai faru da shi kuwa wallahi Sardauna sai ya yi magana, kai sai dai bayan ransa wallahi ba zai taba ganin yana raye a wulakanta matarsa ba. Dalilinta na biyu Kuma Nzeogwu ya harbi Hafsat kafin ya harbi Sardauna, nan ma tace daga nan ne ma na tabbatar da cewa Sardauna ba shi da rai, wallahi yana dai tsaye ne kawai amma Allah ya zare ransa. Tace har Nzeogwu ya harbe shi ba a ji ihunsa ko Kara ko wata magana ba. Hakan ma ya kara tambatar mana da cewa ya rasu.
Jabbo da Goggon Bichi, da Larai Matar Ali Odilin Sardauna wacce itama ganauce sun tabbatar da cewa in ma da wani namiji a sanda abun ya faru to Ali Odili ne.
Matan na Sardauna guda biyu da Larai Matar Ali Odili sun ce duk mazajen dake gidan sun gudu. Sukace duk wani mutum yau daya tara yan Jaridu yace yasan yadda aka kashe Sardauna, ko a gabansa aka kashe Sardauna karya ya keyi.
Marigayi Sheik Abubakar Gumi, shi ne ya yiwa Sardauna wanka ya tabbatar da cewar tabbas akwai harsashi a goshin Sardauna a goshi aka harbeshi.
Bazan iya kawo dukkan hikayoyin a nan ba amma za a iya neman littafi mai suna Jarumar da ba a rubuta ba, Hafsat Ahmadu Bello, wanda Ladi S. Adamu ta rubuta.
