Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta nada Baffa Babba Dan Agundi da Rabi’u Sulaiman Bichi a matsayin Shugaban Kwamitin Rijista na E-Register.
Da yake kaddamar da kwamitin mutum 14 karkashin jagorancin Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya ce sauran mambobin kwamitin sun hada da Abdul Adamu Fagge da Musa Ali Kachako.
Sauran sun hada da Shafi’u Abdullahi Darma, Ahmad Aruwa, Sanusi Sa’idu Kiru Majidadi, Khalid Ishaq Diso, Auwalu Ubale Minjibir, Fa’iz Alfindiki, Binta Rabi’u Spikin, Umar Muhd Rabiu, Muhd Tudun Wada Tweeter da Aminu Umar Dawakin Kudu a matsayin Sakatare. Alhaji Abbas ya bayyana yadda kwamatin zai gudanar da aiki, ya kuma bukaci mambobin kwamitin da su yi aiki tukuru domin ganin an samu nasarar aikin.
Ya ce aikin zai mamaye dukkan mazabun da ke kananan hukumomi 44 na jihar.
