JIGAWA TA SAMU NASARAR KASHI 96 CIKIN 100 YAYIN DA SHIRIN GYARAN TSANGAYA YA FARKO DA DALIBAI MASU TAKARDAR SHAIDA
Gwamnatin Jihar Jigawa ta samu gagarumar nasara a kokarinta na gyaran harkokin ilimi, inda kashi 96 cikin 100 na mahalarta shirin watanni shida na musamman na JISTEB/NBAIS suka cika dukkan ka’idojin da aka gindaya tare da samun takardun shaidar da ake amincewa da su a fadin kasa.
Shirin wanda Hukumar Ilimin Tsangaya ta Jihar Jigawa ta aiwatar tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Karatun Larabci da Addinin Musulunci ta Kasa (NBAIS), ya horas da Alaramma 150 a cibiyoyin karatu da ke Dutse, Hadejia da Gumel.
An koyar da mahalarta darussa guda tara tare da jarrabawa, ciki har da Turanci, Larabci, Addinin Musulunci, Lissafi da kuma Ilimin Kwamfuta, a karkashin tsarin karatu da aka tsara domin hada ilimin addini da na zamani.
Da yake jawabi yayin da Sakatare na Hukumar Tsangaya ya gabatar da rahoton a taron sashen ilimi na wata-wata, Gwamna Umar Namadi ya bayyana matukar jin dadinsa kan sakamakon, inda ya bayyana hakan a matsayin babbar nasara a bangaren ilimi na jihar.
“Alhamdulillah, yau muna cikin farin ciki matuka kan wannan nasara da ‘yan uwarmu suka samu bayan kammala wannan karatu tare da karbar takardun shaida. Kasancewar kusan kashi 96 cikin 100 sun cika dukkan sharuddan da ake bukata ba karamin nasara ba ce,” in ji gwamnan.
Ya kara da cewa nasarar shirin ta nuna irin damar da ke cikin tsarin Tsangaya idan aka ba shi kulawar da ta dace.
“Yanzu kowannensu ya samu abin da zai ba shi damar ci gaba da karatu. A cikin watanni shida kacal an koya musu darussa tara ciki har da Turanci, Larabci da Addinin Musulunci, kuma sun ci jarabawa. Wannan babbar nasara ce.”
Gwamna Namadi ya kuma jaddada muhimmancin wannan nasara, musamman idan aka yi la’akari da asalin mahalartan shirin.
“Ba ko daya daga cikinsu da ya taba zuwa makarantar firamare ta zamani, amma duk da haka sun samu nasarar cin jarabawar da ta kai matakin sakandare. Wannan yana nuna cewa dole ne mu ci gaba da wannan shiri,” in ji shi.
Yayin da ya sake tabbatar da kudirin gwamnatinsa, gwamnan ya ce za a ci gaba da fadada shirin.
“Insha Allah, a matsayinmu na gwamnati, za mu dore da wannan shiri tare da kara inganta shi domin zai kawo mana karin alheri. Haka kuma yana nuna cewa idan muka ci gaba da wannan tsari, zai zama kariya mai karfi gare mu a Jihar Jigawa.”
Gwamnan ya kuma kawo misali na zahiri da ke nuna muhimmancin shirin.
“Akwai wani mahalarta da ya tsaya takara a wani matsayi da ake bukatar takardar sakandare. Da farko bai da ita, amma daga baya ya tuna ya halarci wannan shiri. Ya samo takardarsa kuma aka amince da ita, lamarin da ya ba shi damar samun wannan mukami. Wannan hujja ce karara kan muhimmancin shirin.”
Ya yabawa dukkan masu ruwa da tsaki da suka taka rawa wajen nasarar shirin, ciki har da masu koyarwa, masu tsarawa da kuma Hukumar Ilimin Tsangaya.
“Ina taya ku murna bisa wannan nasara. Wannan aiki ne na hadin kai, kuma yana nuna abin da za a iya cimma idan aka yi aiki tare da gaskiya da jajircewa,” in ji gwamnan.
Rahoton ya kuma bayyana muhimman abubuwan da suka taimaka wajen nasarar shirin, ciki har da hadin kan masu ruwa da tsaki, tsauraran matakan tantance mahalarta, tsara manhajar karatu, samar da masauki da kayan koyo, da kuma ba da lada bisa kwazon mahalarta da masu koyarwa.
Related Posts
Add A Comment
