Bayanda aka ayyana Malam Ibrahim Shekarau Tsohon Gwamnan Jihar kano, Kuma tsohon mimistan ilimi a matsayin mutumin da zai yiwa jam, iyyar Apc takarar kujerar Sanata a yankin kano ta Tsakiya.
Zazzafar Zanga-zangar ce ta ɓarke a Jihar Kano saboda rashin amincewa da Shekarau a matsayin ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a jam’iyyar APC.
AA ZAURA dai yajima yana yiwa jam, iyyar Apc hidima ba tare da kakkautawa ba.
Kungiyoyi a Kano ta Tsakiya sun gudanar da Zanga-Zangar kin amincewa da baiwa Malam Ibrahim Shekarau Takara a APC
Gamayyar kunyoyin da suka haɗa dana Dalibai, Masu Bukhata ta musamman dana Matasa ne dai suka fito kan titi a safiyar wannan rana ta Juma’a domin nuna kin amincewarsuda baiwa tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau takarar sanatan Kano ta tsakiya a Jam’iyyar APC.
Matasan sun taru ne a filin Sukuwa dake Nasarawa GRA, inda suka gabatar da jawabai tare da kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Kano dasu shiga cikin wannan lamari domin A.A Zaura suke bukahata a wannan kujera ba Shekarau ba.
