HUKUMAR FANSHO TA JIHAR JIGAWA TA RABA NAIRA MILIYAN 661 GA MA’AIKATAN DA SUKA YI RITAYA DA IYALAN MA’AIKATAN DA SUKA RASU
Hukumar Fansho ta Gudunmawa ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomi ta fara rabon kudaden hakkokin ritaya da na mutuwar ma’aikata da suka kai Naira 661,162,525.84 ga mutum 272 da suka hada da masu ritaya da kuma iyalan ma’aikatan gwamnati da suka rasu.
Shugaban Ma’aikatan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad K. Dagaceri ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga wadanda suka ci gajiyar tallafin a harabar Pension House da ke Dutse.
Ya bayyana cewa kudaden sun hada da gratuti, hakkokin mutuwa da kuma sauran kudaden fansho na ma’aikatan da suka rasu.
A cewarsa, ma’aikatan 272 sun hada da ma’aikatan gwamnatin jiha, kananan hukumomi da hukumomin ilimi na kananan hukumomi da suka yi ritaya bisa radin kansu ko kuma bayan sun kai shekarun ritaya, da kuma wadanda suka rasu suna bakin aiki.
Dagaceri ya ce za a biya ma’aikata 220 da suka yi ritaya jimillar N519,836,677.71, yayin da iyalan ma’aikata 37 da suka rasu suna bakin aiki za su karbi N123,241,273.10.
Ya kara da cewa rukuni na karshe ya kunshi magadan masu ritaya 15 da suka rasu bayan sun fara karbar fansho na wata-wata kafin cikar mafi karancin shekaru biyar bayan ritaya. Wadannan sun karbi N18,078,575.03.
Shugaban Ma’aikatan ya bayyana cewa tsarin fansho na gudunmawa na jihar Jigawa da kananan hukumomi yana ci gaba da biyan hakkokin masu ritaya da kuma iyalan wadanda suka rasu suna bakin aiki ba tare da tangarda ba.
Haka kuma ya ce tsarin yana biyan dukkan masu ritaya fansho na wata-wata yadda ya kamata a fadin jihar.
A cewarsa, wannan na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da walwalar masu ritaya tare da tabbatar da tsaron rayuwarsu bayan barin aiki.
Tun da farko, Babban Sakataren Hukumar Fansho, Dakta Bilyaminu Shitu Aminu, ya bayyana cewa hukumar ta biya jimillar N3,601,331,427.72 ga masu ritaya 1,428 daga watan Janairun 2026 zuwa yanzu.
Ya ce daga cikin kudaden, an biya ma’aikata 1,161 da suka yi ritaya N2,876,036,977.22, yayin da aka bai wa iyalan ma’aikatan da suka rasu suna bakin aiki N639,800,219.60.
Babban Sakataren ya mika godiyarsa ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, bisa goyon baya da sauye-sauyen da ya kawo tun bayan hawansa mulki.
Ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Umar Namadi ta zuba biliyoyin naira cikin tsarin fansho, lamarin da ya kara karfafa tsarin tare da samar da kwarin gwiwa ga masu ritaya.
Dakta Shitu ya ce tallafin da gwamnatin jihar ta bayar ya yi matukar tasiri wajen karfafa tsarin fansho da tabbatar da dorewarsa.
An gudanar da bikin rabon kudaden a harabar Pension House ta Jihar Jigawa a matsayin wani bangare na kokarin gwamnati na girmama irin gudunmawar da ma’aikatan gwamnati suka bayar yayin aikinsu.
Kudaden za su taimaka wa masu ritaya wajen gudanar da rayuwarsu bayan barin aiki cikin mutunci da kwanciyar hankali.
Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin sun bayyana farin cikinsu kan yadda aka biya su hakkokinsu cikin
