Mataimakin shugaban Najeriyar ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi wajen ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon shugaban ƙasar Janar Yakubu Gowon.
Shettima ya ce sha’awar kayan ya sa ya ɗinkawa shugaba Tinubu amma kuma sai aka samu akasi daga wasu ƴan Maiduguri da ke neman ganin sun haifar da matsala a tsakanin su.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce Tinubu da kan sa ya kira shi, ya kuma faɗa masa abin da mutanen sa suka shaida masa dangane da kayan.
