Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya na Tudun Wada/Doguwa a Jihar Kano, Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya samu amincewar gina sabbin gine-ginen ajujuwa 15 a sassa daban-daban na mazabarsa, domin inganta harkokin ilimi da samar da kyakkyawan yanayin koyo. da koyarwa
An bayyana hakan ne ta hannun sashen yaɗa labarai na ɗan majalisar, a cikin wata sanarwa da aka rabawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Abuja ranar Asabar.
A cewar daraktan yaɗa labaran, ayyukan na daga cikin shirin ayyukan mazabu na shekarar 2026, wanda Hukumar Ilimin Bai-daya ta Kasa (UBEC) ke aiwatarwa a wasu al’ummomi daban-daban da ke cikin mazabar.
Ya ce an tsara ayyukan ne domin magance ƙarancin ajujuwa da kuma samar da ingantaccen muhalli da zai taimaka wa ɗalibai wajen samun ilimi cikin sauƙi.
Daga cikin makarantun da za ,a gina a wuraren da zasu amfana da ayyukan akwai Doguwa Community School, inda ake sa ran sabon ginin ajujuwan zai samar da ƙarin guraben karatu ga ɗalibai.
Sauran wuraren da ayyukan suka shafa sun haɗa da Dadinkowa Community Science School, Asada Secondary School, Murmushi Primary School, Doka Primary/Islamiyya School, da Burji Primary and Islamiyya School.
Haka kuma, ayyukan sun haɗa da Yarmaraya Secondary School, Dalawa Primary School da ke Kasko, Dalawa Katakuri Primary School, da Zega Primary School.
Sauran wuraren da za su amfana sun haɗa da Dakuktkum, Baburi Cikin Gari Community School, da Sabongari Doguwa Islamiyya School, da sauran wurare.
A yankin Burumburum, an kuma tanadi ginin ajujuwa a ƙauyen Shuwi, domin rage matsalar ƙarancin wuraren karatu da al’ummar yankin ke fuskanta.
Daraktan ya bayyana cewa waɗannan ayyuka na daga cikin ayyukan ci gaban mazabar Doguwa na shekarar 2026 a fannin ilimi, yayin da UBEC ke da alhakin aiwatar da su.
Ya ƙara da cewa, a shekarun baya ma, Doguwa ya kasance yana tallafa wa harkokin ilimi a mazabarsa, ciki har da gina ajujuwa da sauran shirye-shiryen da suka shafi inganta samun ilimin bai-daya.
Ana sa ran wannan sabon shiri zai taimaka wajen rage cunkoso a ajujuwan da ake amfani da su a halin yanzu, tare da samar wa malamai da ɗalibai ingantattun wuraren koyarwa da koyo.
Sanarwar ta kuma bukaci al’ummomin da suka amfana da ayyukan da su ba da gudunmawa wajen kula da gine-ginen, domin tabbatar da cewa sun ci gaba da amfani ga al’umma yadda aka tsara.
(NAN)
Related Posts
Add A Comment
