Wani bincike da jaridar muryar Arewa A yau.com,ta gudanar ya gano cewar,an samu karancin masu yawon bude ido a jihar sakamakon babu wasu Al,adu na hausa fulani da makamantansu da jihar jigawa zata yi tunkaho dasu.
Tun daga iyakar jihar jigawa da Bauchi zakaga akwai kabilu Daban -Daban dake zaune a wannan wuraren,kuma mafiya yawansu fulanine sukayiwa jihar kawanya.
Uwa maba da mama jihar kano,itace babbar makwabciya, wadda ake bukukuwan nuna Al,adu, ajiha jigawa,ne yakamata a yi bukukuwan hujin shanu bikin shan kabewa da wasan wanzamai da shadi da Dambe da kokawa da wasan langa da shankabewa da kamun kifi,da sauran mahimman bukukuwan wasanni gargajiya.da ka iya jawo hankalin masu zuba jari da yawon bude idanu a jihar,uwa uba ma dai,azamanance hatta kwallon kafa da ake bugawa,da ake cewa inter local government,ba a taba kirkiraba,balle a ce an yi a samu karuwar Arziki,ma,ana tun daga kan masu saida gyada da dan wake da rake da waina da masu ababan hawa tsire,su sami karuwar Arziki
Jihar jigawa jihace da ta shahara a fannin noma da kiwo, da kuma Albarkatun karkashin kasa,wadda zata iya gogayya da kowacce jiha,
Amma a yau ba sai gobe ba jihar jigawa ba,a jiyo a monta a yankin Afrika, wadda jihar jigawa tayi iyaka da kasar nijar,harma da auratayya da kasuwanci mai KARFI ya shiga tsakani,mai dorewa.
Akwai bukatar a dinga yayata Ayyukan jihar jigawa da kuma gudanar da sabbin kirkire kirkire daga ma,aikatar Al,adu da jin dadin matasa, wadda zata tafi da harkokin yada labarai, domin jihar jigawa ta samu tagomashi na masu saka jari.
Akwanakin baya, Gwamnan jihar jigawa Malam Umar Namadi Danmodi ya gayyato,masu saka jari ko a fannin noman Dabino,wadda hakan na nuni da Babban Nasara ce da zata taimaka a samu karuwar Arziki tun daga tushe baya ga ma,aikata da zasu amfana da sauran masu karamin karfi,
Kuma ya kamata ma,aikatar yada labarai ta jihar karkashin kwamishinan yada labarai ta zage Damtse ta fito tayi aiki tukuru domin yayata jihar jigawa a Duniya tamkar yadda waiya yakeyi a jihar kano,Domin kuwa babu sahihin bayanin dake nuni da cewar akwai ma,aikatar yada labarai da kwamishinan yada labarai yake gudanar da Ayyukan cigba na Gwamnan jihar,hasali ma idan maki ake bayarwa sai dai ka bashi tayar mota, sakamakon nakasu da ake samu wajen yayata wa da kirkirar Ayyukan cigba na Gwamnan jihar jigawa.
Idan hali yayi zamu Dora daga wajen da muka tsaya wannan ra,ayine na jaridar muryar Arewa A yau.com
