Mai neman takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai neman wakiltar mazabar Dukku/Nafada,a Jihar Gombe, Hon. Umar Ahmed Nafada, ya bayyana a gaban kwamitin tantance ‘yan takara na jam’iyyar APC domin gudanar da tantancewa gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Bayan gabatar da dukkan takardun da ake bukata tare da amsa tambayoyin da kwamitin tantancewar ya yi masa, Hon. Umar Ahmed Nafada ya samu nasarar tsallake tantancewar domin shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Nasarar tantancewar ta tabbatar da cewa Hon. Umar ya cika dukkan sharuddan kundin tsarin mulki da na jam’iyya da ake bukata domin neman amincewar al’ummar mazabar Dukku/Nafada, a Jihar Gombe.
. HHon afada mutum ne da ya yi wakilci a majalisar wakilai ta tarayya, daga bisani ya zama shugaban ma, aikatan shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai na tarayya Rt Hon Alhassan Ado Doguwa,.
Haka kuma ya kasance Mai Bada shawara ga Ministan Harkokin sufuri na kasa.
