Jam’iyyar APC Ta Sake Tsayar da Gwamna Namadi a Matsayin Dan Takarar Gwamna, Ta Bukaci Nasarar Duk ‘Yan Takara a 2027
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Jigawa ta sake tabbatar da Gwamna Malam Umar Namadi a matsayin dan takarar gwamna na bai daya domin zaben shekarar 2027, yayin da gwamnan ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar a fadin jihar da su fara cikakken shiri da wayar da kai domin tabbatar da nasarar dukkan ‘yan takarar APC a zaben mai zuwa.
An gudanar da taron tabbatarwar ne ranar Asabar a Filin Wasan Dutse Township Stadium, inda dubban magoya bayan APC daga kananan hukumomi 27 na jihar suka halarta tare da shugabannin jam’iyya, dattawa, masu ruwa da tsaki da zababbun jami’ai.
Daga cikin manyan bakin da suka halarci taron akwai tsofaffin gwamnonin Jigawa, Barista Ali Sa’ad Birnin Kudu da Alhaji Ibrahim Saminu Turaki; tsohon mataimakin gwamna kuma mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia; ‘yan majalisar dokoki ta kasa; ‘yan majalisar dokokin jihar; shugabannin jam’iyya da sauran manyan ‘yan siyasa daga sassan jihar.
Haka kuma jami’an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da wakilan hukumomin tsaro sun halarci taron.
Da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar bayan tabbatar da shi, Gwamna Umar Namadi ya gode wa Allah Madaukakin Sarki tare da nuna jin dadinsa ga ‘ya’yan APC da al’ummar Jigawa bisa amincewar da suka sake nuna masa.
“Alhamdulillah, muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya raya mu muka shaida wannan rana. Ina mika godiya ta musamman ga al’ummar Jigawa, musamman mambobin jam’iyyarmu ta APC, bisa amincewa da ni a matsayin dan takarar gwamna na zaben 2027,” in ji shi.
Gwamna Namadi ya bayyana cewa wannan goyon baya babban nauyi ne, inda ya tabbatar wa magoya bayan jam’iyyar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen aiwatar da ayyukan ci gaba da inganta rayuwar al’umma a fadin jihar.
Ya kara da cewa kudirin gwamnatinsa na “Greater Jigawa” yana kan turba madaidaiciya, kuma zai ci gaba da zama jagora wajen tsara manufofi da shirye-shiryen gwamnati.
“Aikinmu na Greater Jigawa yana tafiya yadda ya kamata, kuma za mu ci gaba da kokarin ganin mun kai shi ga nasara baki daya,” in ji gwamnan.
Sai dai ya bayyana cewa wannan mataki shi ne farkon tafiyar siyasa zuwa 2027, inda ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da su ci gaba da hadin kai da jajircewa domin samun nasarar APC baki daya.
“Da wannan dama da kuka ba ni, mun kammala mataki na farko ne kawai. Yanzu ya kamata mu hada kai domin tabbatar da cewa dukkan ‘yan takarar APC daga shugaban kasa har zuwa ‘yan majalisar dokokin jihar sun samu nasara a zaben 2027,” in ji Gwamna Namadi.
Ya yabawa dattawan jam’iyya da masu ruwa da tsaki bisa yadda suka gudanar da tsarin maslaha cikin lumana da nasara, yana mai cewa hakan ya nuna hadin kai da kwarewar shugabannin APC a Jigawa.
Gwamnan ya ce kusan kashi 90 cikin 100 na tsarin maslahar APC a Jigawa ya samu nasara, tare da yaba wa shugabanni da dattawan jam’iyyar bisa jajircewa da sadaukarwar da suka yi domin cimma wannan buri.

Haka kuma ya yi yabo na musamman ga tsohon gwamnan Jigawa, Barista Ali Sa’ad Birnin Kudu, bisa jagorantar tuntuba da hada kan masu ruwa da tsaki a dukkan kananan hukumomin jihar.
Gwamna Namadi ya kuma gode wa dattawan jam’iyyar bisa ci gaba da bayar da shawara da goyon baya duk da yawan ayyukansu da nauye-nauyen da ke kansu.
“Muna matukar godiya da irin sadaukarwar da dattawanmu suke yi da kuma shawarwarin da suke ci gaba da ba mu. Za mu ci gaba da dogaro da su wajen tabbatar da hadin kai da nasarar jam’iyyarmu a Jigawa,” in ji shi.
