Acikin wata sanarwa da shugaban rikon kungiyar ya bayar Alh Umar faruk musa ya bayyana cewar kungiyar tayi rashin Tsohon shugaban kungiyar Kuma Uba.
Alh salisu Aliyu Rano ya rike kungiyar masu gidajen bulo da dangoginsa yayinda yayi kokari ya kaita mataki na gaba kafin rasuwar sa.
A saboda haka nema shugaban rikon kungiyar eng Umar faruk musa ya mika sakon ta,aziyyar yayan kungiyar ga iyalai da Yan, uwa da Abokan Arziki,
Eng Umar faruk yayi Addu,ar ALLAH ya JIKAN sa ALLAH ya yafe masa, ALLAH ya baiwa iyalai hakurin jure wannan rashi
Tuni dai akayi Jana,izar sa a yankin yan kusa dake karamar hukumar Kumbotso
