Abbas Ibrahim Ya Zama Ɗan Takarar Mataimakin Gwamnan Kano na Labour Party
Daga Jamila Abdullahi – DMM Media
Tsohon Shugaban Ƙungiyar ’Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kano, Comrade Abbas Ibrahim, ya samu tikitin tsayawa takarar Mataimakin Gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2027 mai zuwa.
Abbas Ibrahim, wanda fitaccen ɗan jarida ne kuma tsohon shugaban NUJ a Kano, ya bayyana sabon matsayinsa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayyana aniyarsa ta ɗaukar wannan sabon nauyi na siyasa.
Bayan samun tikitin takarar Mataimakin Gwamna, Abbas Ibrahim ya kuma sanar da murabus ɗinsa daga matsayin National Trustee na NUJ, Zone A, domin ba da cikakken lokaci da kulawa ga sabon aikin siyasar da aka ɗora masa.
Ya ce ya yanke wannan shawara ne domin samun damar mayar da hankali sosai kan sabon nauyin da ke gabansa, tare da ba shi damar taka rawa kai tsaye a harkokin siyasa.
A cikin sanarwar tasa, Abbas Ibrahim ya ce: “Cikin tawali’u, godiya da jinjina ga ’yan uwana abokan gwagwarmaya, ina sanar da ku cewa, bayan fitowata a matsayin ɗan takarar Mataimakin Gwamna na Labour Party da aka sake fasalin ta a Jihar Kano, na yanke shawarar yin murabus daga matsayina na National Trustee na NUJ, Zone A.”
Ya ƙara da cewa haɗa nauyin da ke kansa na National Trustee na NUJ da sabon aikin siyasa zai buƙaci lokaci, himma da kulawa mai yawa. Saboda haka, ya ga ya dace ya sauka daga mukamin NUJ domin ya mayar da hankali sosai kan sabon aikin da aka ɗora masa.
Tsohon shugaban NUJ na Kano ya kuma nuna godiya ga abokan aikinsa, ’yan jarida da sauran abokan gwagwarmaya bisa irin goyon baya da haɗin kai da suka ba shi a tsawon lokacin da ya shafe yana aiki a fannin aikin jarida.
Fitowar Abbas Ibrahim a matsayin ɗan takarar Mataimakin Gwamna ta ƙara wani sabon salo cikin harkokin siyasar Jihar Kano, musamman yayin da ake ƙara samun shirye-shirye da tuntuba tsakanin jam’iyyun siyasa da masu neman takara gabanin babban zaɓen 2027.
Matakin da Abbas Ibrahim ya ɗauka ya kuma nuna sauyin da ya samu daga dogon lokaci da ya shafe yana jagoranci da gudanar da ayyuka a cikin ƙungiyar ’yan jarida, zuwa shiga fagen siyasar jam’iyya kai tsaye, inda ake sa ran zai taka muhimmiyar rawa wajen ayyukan siyasa da yaƙin neman zaɓen Labour Party a Jihar Kano.
A halin yanzu, Labour Party na ci gaba da shirye-shiryenta da tuntubar masu ruwa da tsaki, yayin da Jihar Kano ke ƙara matsowa kusa da babban zaɓen shekarar 2027.
