Tinubu ya jajanta wa al’ummar Borno kan hare-haren ta’addanci a Maiduguri
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya jajanta wa al’ummar jihar Borno kan hare-haren ta’addanci da suka afku a Maiduguri, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici matuka.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Talata, Tinubu ya nuna alhininsa ga wadanda suka rasa rayukansu, tare da tausaya wa wadanda suka jikkata, yana kuma nuna goyon bayansa ga daukacin al’ummar jihar Borno a wannan lokaci mai wahala.
Ya bayyana cewa hare-haren da ake kaiwa na baya-bayan nan wani yunƙuri ne na karshe daga masu aikata laifuka da ‘yan ta’adda domin yada tsoro, yana mai cewa ana ci gaba da matsa musu lamba daga rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro.
Shugaban kasar ya jaddada kudurin gwamnatinsa na ci gaba da kara kaimi wajen yaki da dukkan masu aikata laifuka a duk inda suke a fadin kasar.
Tinubu ya kuma yaba da jarumtaka da kwazon sojojin Najeriya, yana mai cewa sun samu nasarar dakile hare-haren hadin gwiwa da ‘yan ta’adda suka kai kan sansanonin soji a jihar.
Ya kara da cewa hare-haren da suka faru a ranar Litinin na daga cikin ayyukan karshe na kungiyoyin ta’addanci masu mugunta, yana mai cewa jami’an tsaro da kungiyoyin sa kai za su dauki matakin da ya dace domin murkushe su.
