An bayyana Mutunta Malamai a Matsayinsu na masu bada Gudunmawa a cikin Al’uma da cewa abu ne da yazama wajibi.
Shugaban kungiyar Movement Teachers Foward Sola Adeola Amudipe shine ya bayyana hakan a wani Taron manema Labarai da kungiyar ta gabatar.

Yace a yanzu makomar Kasar Nan tana hannun Malamai domin kasancewarsu jagorori ne a cikin Al’uma.
Sola Adeola ya kara da cewa Sun gabatar da Taron manema Labaran ne bisa yadda a yanzu akayi watsi da nuna halin ku in kula da Makomar Malamai a wannan Kasa.
Inda yace ya Zama wajibi a samu canji domin ceto bangaren ilimi da Kuma dalibai Masu tasowa a Kasar Nan.
Shugaban kungiyar Yace idan har da gaske anason cigaban Kasar nan to Dole a kula da cigaban Malamai a kowanne mataki.
Kamar yadda yace bawai kawai an tara Malamai ne domin ayi taro aga juna ba, anyi Taron ne domin yunkurin samun mafita da Kuma cigaban Malamai.
Taron kazalika bawai ya tsayar ga neman Makomar Malamai da samun Mafitarsu ba harma da neman sake fasalin Koyarwa a jihohi 36 harda babban Birnin Tarayya Abuja.

