EFCC ta kama fitacciyar jarumar Kannywood, Samha Inuwa kan zargin wulakanta takardar Naira
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kama fitacciyar jarumar Kannywood, Samha Inuwa, bisa zargin wulakanta kudin Najeriya, wato naira.
Jami’an EFCC na shiyyar Kano ne suka kama jarumar a ranar Talata, 3 ga watan Fabrairu, 2026, bayan yaduwar wani bidiyo a kafafen sada zumunta wanda ake zargin ya nuna jarumar tana amfani da takardun naira wajen goge majina daga hancinta.
A cewar hukumar, yaduwar bidiyon ne ya sa ta dauki matakin gaggawa, inda ta bi diddigin jarumar tare da cafke ta domin yi mata tambayoyi kan lamarin.
EFCC ta bayyana cewa a halin yanzu ana tsare da Samha Inuwa a cibiyar tsare mutane ta hukumar yayin da bincike ke ci gaba da gudana.
Hukumar ta kara da cewa za a gurfanar da wacce ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.
