KOMC ta bukaci ’yan jarida su kiyaye da’a, ta amince da gudummawar wata-wata
KANO: Ƙungiyar ’Yan Jaridun Yanar Gizo ta Kano Online Media Chapel (KOMC) ƙarƙashin Ƙungiyar ’Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), ta buƙaci mambobinta da su riƙa bin ƙa’idojin aikin jarida, musamman wajen tabbatar da sahihanci, adalci da ɗaukar rahotanni cikin haƙƙin da ya dace, musamman yayin ɗaukar labaran siyasa da zaɓe.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a yayin babban taronta da aka gudanar ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2026, a Cibiyar ’Yan Jarida ta NUJ da ke Kano, inda mambobin suka tattauna batutuwan da suka shafi ƙa’idojin aikin jarida, walwalar mambobi, hanyoyin samun kuɗaɗen gudanarwa, shugabanci da ci gaban ƙungiyar baki ɗaya.
A cikin sanarwar da aka fitar bayan taron, majalisar ta jaddada muhimmancin bin ƙa’idodin aikin jarida na NUJ tare da tabbatar da ƙwarewa a dukkan ayyukan da mambobi ke gudanarwa.
An kuma buƙaci ’yan jaridun da su tabbatar da sahihanci, daidaito, adalci da ɗaukar nauyin alhakin da ke kansu wajen gudanar da rahotanni, tare da fifita zaman lafiya da muradun jama’a musamman wajen ɗaukar labaran zaɓe da sauran batutuwan siyasa masu matuƙar muhimmanci.
Taron ya kuma yi kira ga mambobi da su guji duk wani aiki da ka iya rage darajar ko amincin aikin jarida, tare da jaddada muhimmancin gudanar da aikin jarida cikin ɗa’a a kafafen yaɗa labarai na yanar gizo.
An amince da gudummawar wata-wata
Dangane da hanyoyin tabbatar da dorewar harkokin kuɗi na ƙungiyar, taron ya amince da fara karɓar gudummawar kuɗi a kowane wata daga mambobi, domin ƙarfafa tushen kuɗaɗen shiga da kuma taimaka wa ayyuka da shirye-shiryen ƙungiyar.
Haka kuma, taron ya amince baki ɗaya da kafa wani kwamitin tara kuɗaɗen shiga mai mambobi bakwai, wanda zai nemi tare da bibiyar halastattun hanyoyin samun kuɗaɗen shiga masu ɗorewa ga ƙungiyar.
Kwamitin zai duba damar ƙwararrun ayyuka, haɗin gwiwa da sauran hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da suka dace da doka, waɗanda za su taimaka wajen gudanar da ayyukan ƙungiyar da kuma inganta harkokin ofishinta.
Sai dai taron ya jaddada cewa duk wani yunƙuri na neman kuɗaɗen shiga dole ne ya kasance cikin daidaito da nauyin da ke kan ’yan jarida da kuma ƙa’idojin ɗa’ar aikin jarida.
An jaddada haɗin kai da walwala
KOMC ta kuma buƙaci mambobinta da su ƙara ƙarfafa haɗin kai, mutunta juna da taimakon juna, tana mai cewa ci gaban ƙungiyar ya dogara ne da irin gudummawar da kowane ɗan uwa zai bayar.
A kan walwalar mambobi da harkokin gudanarwa, taron ya tattauna batun samar da katunan shaidar zama mamba ga ’yan ƙungiyar, inda aka yanke shawarar tuntuɓar Majalisar NUJ ta Jihar Kano domin bin hanyoyin da suka dace har zuwa Babban Sakatariyar Ƙungiyar ta Ƙasa.
Haka kuma, taron ya amince da samar da tsarin “Red Card” ga mambobin da ke gudanar da harkokin tallace-tallace, domin samun ingantaccen tsari wajen tantancewa da daidaita mambobin da ke karɓar ko gudanar da ayyukan tallace-tallace a madadin kafafen yaɗa labarai na yanar gizo da suke aiki da su.
Za a gudanar da bikin cikar shekara biyu
Taron ya kuma amince da gudanar da bikin cikar ƙungiyar shekaru biyu, maimakon shawarar farko ta gudanar da bikin cikar shekara ɗaya.
Ƙungiyar ta yi kira ga mambobi da sauran masu ruwa da tsaki da su ƙara amfani da ofishin ƙungiyar, shirye-shiryenta da ayyukanta na hukuma, tare da jaddada muhimmancin gudanar da tarurruka akai-akai da kuma gabatar da rahotannin sakatariya da na kuɗi yadda ya kamata.

Taron ya yaba wa shugabancin ƙungiyar bisa gabatar da ingantattun rahotannin sakatariya da harkokin kuɗi, tare da sake jaddada aniyar ƙungiyar na ƙarfafa aikin jarida na ƙwararru, inganta ɗaukar rahotanni cikin ɗa’a, bunƙasa walwalar mambobi da ƙara ƙwarewa da ci gaban ’yan jaridun kafafen yaɗa labarai na yanar gizo a Jihar Kano.
Taya Gwamna Abba murna
A wani ɓangare na sanarwar, taron ya taya Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, murna bisa karramawar da Ƙungiyar NUJ ta yi wa Gwamnan yayin wani taron bitar da aka gudanar a Jihar Jigawa.
An ce daga bisani Gwamnan ya karɓi wannan karramawa yayin taron Majalisar Zartarwar Jihar Kano.
Shugaban KOMC, Comrade Abubakar Abdulkadir Dangambo, da Mataimakin Sakatare, Comrade Sunusi Kofar Na’isa, ne suka sanya hannu kan sanarwar.
Kwamitin da ya tsara sanarwar ya ƙunshi Comrade Hamman Abdulkareem a matsayin Shugaba, Comrade Sani Magaji Garko a matsayin Sakatare, da Comrade Salisu Babangida a matsayin mamba.
