Alokacinda masu yin sharhi ga abinda kanje ka komo a kan yadda ake gudanar da harkokin kasuwancim man fetur, da yadda ake jallaku jalle da cigaban Mai harkar rijiya ga Kaya a garinku Amma yafi karfin Mai karamin karfi kwatsam matatar man Dangote ta sanya Al, ummar Nijeriya cikin yanayin fuska biyu bakin ciki da bacin rai wani lokacin kuma ayi Rabin farin ciki saboda abin babu dadi tamkar abinnan da ake cewa ga koshi ga kwanan.
Matatar man Dangote ta kara farashin man fetur da Naira 75 kan Kowacce Lita yayin da farashin ya tashi daga naira, naira 1200 zuwa naira 1275, wannan lamari na Kara jefa Al, ummar kasa Nijeriya cikin yanayin talauci da kaskanci. Yan kasuwa dake dillancin man fetur da gidajen Mai sun nuna damuwa bisa yadda wannan Karin kudi ka iya sake tada zaune tsaye domin kuwa Akwai masu Ababan hawa da dama da suka ajiye sakamakon rashin tabbas ga manfetur yadda yake hawa yake sauka.
Farashin Mai Ya Ƙara Tashi — Shin Wannan Shi Ne Farkon Wata Sabuwar Matsala?
Matatar Dangote Refinery ta sake ɗaga farashin man fetur (PMS) daga ₦1,200 zuwa ₦1,275 kowace lita — wani mataki da ya sake girgiza kasuwar mai a Najeriya. Rahotanni sun nuna cewa:
* An ɗan dakatar da sayar da mai na wani lokaci
* Dalilin haka na da alaƙa da matsala a tsarin Proforma Invoice da ke shafar jigilar kaya
* Ƙarin tashin farashi a gidajen mai
* Ƙarin wahala ga talakawa
* Tashin farashin abinci da sauran kayayyaki Masu nazari na cewa:
Idan ba a warware matsalar cikin gaggawa ba, akwai yiwuwar farashin zai ci gaba da tashi, wanda zai ƙara tsananta tsadar rayuwa a ƙasar.
A ganinku, wannan karin farashi zai tsaya nan ne, ko kuwa har yanzu akwai ƙarin tashin da ke tafe
