Jami’an ’yan sanda sun kai samame hedikwatar JKD Television da Hamada Radio da ke Millennium City a Kaduna, inda suka kama Manajan Daraktan kamfanin, Charles Abah, da wani jami’in tsaro.
An kai samamen ne bayan wani faifan bidiyo da JKD ta watsa kan Ibrahim Kabir Masari, mai bai wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin siyasa.
Rahotanni sun ce jami’an ’yan sandan sun shiga harabar kamfanin ne suna neman ’yar jarida Zainab Salihu Yabagi, wadda ta gabatar da shirin, kafin daga bisani su kama ma’aikatan biyu.
A halin yanzu, ana tsare da Charles Abah da jami’in tsaron a hedikwatar rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna.
Editan-in-Chief na JKD, Muhammad Sani Aliyu, ya yi Allah-wadai da kamen, yana mai bayyana shi a matsayin barazana ga ’yancin aikin jarida.
Aliyu ya kuma zargi cewa an shirya kamen ne bisa umarnin Ibrahim Kabir Masari, inda ya bukaci a gaggauta sakin ma’aikatan biyu.
Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ba ta bayyana dalilin kama mutanen biyu ko irin laifin da ake zarginsu da aikatawa ba.
Ana iya cewa irin batunnanne na kilu taja bau
