Daga Ibrahim Muhammad Dantata
Ɗan Shekara 60 Ya Mutu A Hotel Bayan Ya Shiga Da Matashiya Ƴar Shekaru 20
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce ta fara gudanar da bincike kan mutuwar wani mutum mai shekara 60 da ya rasu a wani otal da ke birnin Dutse a ranar Talata, 21 ga Yuli, 2026.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa marigayin ya shiga otal ɗin tare da wata mata mai shekara 20. A cewarsa, mutumin ya fara fama da matsalar numfashi bayan ya nemi abinci.
Sanarwar ta ce an garzaya da shi Babban Asibitin Dutse, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa. Rundunar ta kuma bayyana cewa an samu wasu nau’ikan abinci, abubuwan sha, kayayyakin marigayin da kuma wani sinadari da ake zargin na ƙarfin maza ne a cikin ɗakin otal ɗin.
‘Yan sanda sun ce an miƙa gawar mamacin ga iyalansa domin gudanar da jana’iza, yayin da matar da ta kasance tare da shi ke ci gaba da bai wa jami’an bincike haɗin kai.
Rundunar ta buƙaci al’umma da su guji yaɗa jita-jita ko bayanan da ba a tabbatar da su ba, tana mai jaddada cewa bincike kan lamarin na ci gaba.
“Wannan lamari abin tausayi ne kuma ya kamata ya zama darasi ga al’umma baki ɗaya. Idan har rahotannin da aka fitar suka tabbata, yana nuna muhimmancin ƙarfafa tarbiyya, kula da iyalai, da kuma tabbatar da bin doka da oda a cikin al’umma.
A matsayinmu na al’umma Masu aiki da Sharia ta musulunci, ya dace hukumomi su ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace wajen kare ɗabi’u da hana wurare su zama mafakar aikata ayyukan da suka saɓa wa addini da dokokin ƙasa.
Ya kamata iyaye su ƙara sanya ido kan tarbiyyar ‘ya’yansu, yayin da masu gudanar da otal-otal da sauran wuraren kwana su tabbatar da bin ƙa’idojin tsaro da dokoki domin hana amfani da wurarensu wajen aikata munanan ayyuka.
Muna roƙon Allah Ya gafarta wa mamacin, Ya kare al’ummarmu daga fitintinu da lalacewar ɗabi’u, Ya kuma ba hukumomi ikon gudanar da cikakken bincike cikin adalci da gaskiya.
