BITAR TSARIN RABA KUDADEN SHIGA: GWAMNA NAMADI YA BAYYANA FATAN SAMUN ADALCI A AIKIN RMAFC
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana fatansa cewa bitar tsarin rabon kudaden shiga na Najeriya da Hukumar Tattara Haraji da Rabon Kudade ta Kasa (RMAFC) ke shirin gudanarwa za ta gudana cikin gaskiya, adalci da daidaito ga dukkan jihohi da masu ruwa da tsaki.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar bakuncin tawagar hukumar karkashin jagorancin Barrista Imo Effiong Akpan, Kwamishinan Tarayya mai wakiltar Jihar Akwa Ibom, a gidan gwamnatin jihar da ke Dutse.
Tawagar ta kai ziyarar ne domin kaddamar da aikin tantance bayanai na kasa baki daya da hukumar ke gudanarwa a fadin tarayya a matsayin wani bangare na bitar tsarin rabon kudaden shiga.
Gwamna Namadi ya bayyana aikin a matsayin wanda ya dace kuma ya zama wajibi duba da sauye-sauyen tattalin arziki da zamantakewa da ake fuskanta a kasar nan, tare da yabawa hukumar bisa daukar wannan mataki.
Ya ce, “Muna da yakinin cewa za a yi adalci a wannan aiki. Mun yi imani cewa za a yi wa kowa adalci bisa ka’idojin da ake bukata.”
Gwamnan ya kara da cewa yunkurin da aka yi a baya na sake duba tsarin rabon kudaden shiga bai kai ga nasarar da ake bukata ba, amma ya nuna kwarin gwiwa cewa shugabannin hukumar na yanzu za su samu nasarar gudanar da aikin.
Ya ce, “Yunkurin da hukumar ta yi na sake duba tsarin rabon kudaden shiga abin yaba ne saboda an yi kokari da dama a baya ba tare da samun nasara ba.”

“Amma bisa jajircewar da shugabannin hukumar na yanzu suka nuna, muna da kyakkyawan fata cewa wannan aiki zai yi nasara, Insha Allah.”
Gwamna Namadi ya kuma tabbatar wa hukumar da cikakken goyon baya da hadin kan gwamnatin jihar Jigawa a duk tsawon lokacin gudanar da aikin.
Tun da farko, Barrista Imo Effiong Akpan ya bayyana cewa aikin tantance bayanan na kasa baki daya yana da nufin tabbatar da cewa bayanan da ake amfani da su wajen rabon kudaden shiga sun dace da halin da ake ciki a yanzu a fadin tarayya.
Ya ce sauye-sauyen yawan jama’a, fadada ababen more rayuwa da kuma ci gaban jihohi sun sanya ya zama wajibi a rika yin bitar bayanai lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da adalci da daidaito wajen rabon arzikin kasa.
Barrista Akpan ya kuma tabbatar wa gwamnan cewa za a gudanar da aikin cikin kwarewa, gaskiya da rikon amana bisa ka’idojin aiki na zamani.
