Gwamnatin Jihar Kano Ta Sanar da ƘarshenZango na Uku na Shekarar Karatu
Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta sanar da iyaye, masu kula da yara, masu makarantu da kuma al’ummar jihar cewa, zangon karatu na uku na shekarar karatu ta 2025/2026 zai kawo ƙarshe a dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da ke faɗin jihar.
Bisa ga jadawalin shekarar karatu da aka amince da shi, makarantun kwana-kwana (Day Schools) za su rufe ranar Jumma’a, 31 ga Yuli, 2026, yayin da makarantun kwana (Boarding Schools) za su rufe ranar Asabar, 1 ga Agusta, 2026.
Ma’aikatar ta kuma sanar da cewa, sabon zangon karatu na shekarar 2026/2027 zai fara ne ranar Lahadi, 7 ga Satumba, 2026, ga ɗaliban makarantun kwana, yayin da makarantun kwana-kwana za su koma karatu ranar Litinin, 8 ga Satumba, 2026.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Gwani Dakta Ali Haruna Abubakar Makoda, ya taya ɗalibai, malamai, shugabannin makarantu da iyaye murnar kammala wata shekarar karatu cikin nasara. Ya yaba da jajircewarsu, haƙurinsu da haɗin kan da suka bayar a tsawon shekarar, wanda ya taimaka wajen bunƙasa harkokin ilimi a jihar.
Kamar yadda Babban Daraktan sashen wayar da kan da ilimantarwa,na ma,aikatar,malam musbahu yakasai ya sanyawa hannu
Haka kuma, Kwamishinan ya buƙaci iyaye da masu kula da yara su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun yi amfani da hutu makaranta ta hanyar gudanar da ayyukan ilimi, tarbiyya da nishaɗi masu amfani domin ƙara inganta iliminsu da halayensu.
Ya kuma shawarci masu makarantu da su yi amfani da lokacin hutun wajen gyaran gine-gine da kayan aiki, tare da kammala shirye-shiryen da suka dace domin fara sabon zangon karatu cikin nasara.
A ƙarshe, Kwamishinan ya yi wa ɗalibai da duk masu ruwa da tsaki a harkar ilimi fatan samun hutu cikin zaman lafiya, tsaro da albarka, tare da fatan samun nasarar fara shekarar karatu ta 2026/2027.
