Hukumar yaƙi da rashawa a Najeriya ICPC na tuhumar shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin tarayya Femi Gbajabiamila, kan taƙaddamar ma’aikatar bogin nan da ake zargin an ƙirƙira a ƙasar.
Adeniyi Adeyemi, wanda ke shugabantar ma’aikatar, ya yi iƙirarin bai wa Gbajabiamila naira miliyan 400 a matsayin kuɗin sayen muƙamin nasa.
Kasancewarsa babban hadimi a fadar shugaban kasa, wannan yasa ana yi masa zargin badakala iri daban -daban da suka hada da zargin cin hanci da handama da baba kere da,sanya shinge tsakanin shugaban kasa da talakawa
