Wani Rubutu da Mai taimakawa Hon Alhassan Ado Doguwa Akan Yada Labarai ya rubuta a shafinsa na kafar sadarwa ta face book
Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa Ya Halarci Tantancewar ‘Yan Takarar APC a Abuja
Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa (OON), wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Majalisar Yankin Arewa, ya halarci zaman tantancewar ‘yan takara da mambobin jam’iyyar APC a ranar Asabar, 9 ga watan Mayun 2026 a Abuja.

Shugabar Kwamitin Tantancewa na Panel B ita ce Sanata Uche Ekwunife ta jam’iyyar APC daga Jihar Anambra. Rahotanni sun bayyana cewa Sanata Uche Ekwunife ta taba kasancewa abokiyar aiki da Rt. Hon. Doguwa a Majalisun Tarayya na 5 da na 6.
An gudanar da tantancewar ne a Treasure Hotel da ke Abuja, inda Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa ya samu nasarar kammala aikin tantancewar cikin nasara.
Da yake bayyana farin cikinsa bayan tantancewar, Doguwa ya gode wa Allah Madaukakin Sarki bisa nasarar da aka samu, inda ya ce “Alhamdulillah” bisa yadda komai ya gudana lafiya da nasara.