Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daga yankin ƙaramar hukumar Doguwa karkashin jagorancin Malam musa Salihu Ririwai, sun nuna goyon baya tare da Amincewa da Rt Hon. Alhassan Ado Doguwa yayi tazarce domin ya sake tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya.
Cikin wata sanarwa da Shugaban Caucus na jam, iyyar Apc daga Doguwa, Hon. Musa Salihu ya yi, ya ce an cimma wannan matsaya ne bayan wani taro da suka gudanar domin tattauna makomar siyasar yankin da kuma wanda zai wakilce su.
Ya ƙara da cewa sun amince da Ado Doguwa ne saboda irin ƙwarewa da gogewarsa a majalisa, tare da irin gudunmawar da yake bayar wajen ci gaban al’ummar mazabar.
Haka kuma, ya jaddada cewa masu ruwa da tsakin sun yi alkawarin mara masa baya gaba ɗaya domin tabbatar da nasararsa a zaɓen da ke tafe..
