Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta ce jami’anta sun ceto mutane goma daga cikin fasinjojin wata motar bas da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin dajin Falgore da ke Ƙaramar Hukumar Doguwa.
Rundunar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar 26 ga Yulin 2026, lokacin da wasu mutum biyar ɗauke da adda da bindiga suka tare wata motar Toyota Hiace mai lambar BKK 6824 XA da ke kan hanyarta daga Jos zuwa Kano, tsakanin Gate Two Safer Highway da Dogo Dutse.
A cewar rundunar, maharan sun yi garkuwa da mutum 13 daga cikin fasinjoji 20 da ke cikin motar. Sai dai bayan samun rahoton lamarin, jami’an ‘yan sanda na sashen Doguwa sun garzaya wurin tare da jami’an musamman, inda suka yi musayar wuta da maharan, lamarin da ya kai ga ceto mutum tara, yayin da wani namiji ya tsere daga hannun masu garkuwar.
Rundunar ta ce har yanzu mutum uku, ciki har da namiji ɗaya da mata biyu, na hannun masu garkuwa. An kai waɗanda aka ceto Asibitin Gwamnatin Doguwa domin kula da lafiyarsu, yayin da rundunar ta ce ta ƙara ƙaimi wajen gudanar da samame da bincike domin ceto sauran mutanen da kuma cafke maharan.
