SABON KWAMANDAN NSCDC NA JIHAR NEJA YA KARƁI RAGAMAR AIKI
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ya fitar DSC Rabiu muti Sabon Kwamandan Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) reshen Jihar Neja, Commandant Abdulhamid Salisu Kabara, ya karɓi ragamar jagorancin hukumar a jihar, bayan ya karɓi aiki daga hannun tsohon Kwamandan, Commandant Suberu Siyaka Aniviye.
A wata sanarwa da Kakakin Rundunar, DSC Abubakar Rabiu Muti, ya sanya wa hannu, ta ce sabon Kwamandan ya karɓi aiki ne a wani lokaci mai matuƙar muhimmanci ga hukumar, musamman bayan rasuwar mutane 37 da aka kama bisa zargin hannu a ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a jihar.
Commandant Kabara ya bayyana matuƙar alhini da jimami kan asarar rayukan, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu da dukkan waɗanda wannan mummunan lamari ya shafa.
Ya ce duk da cewa NSCDC na ci gaba da gudanar da ayyukanta na doka da suka haɗa da kama waɗanda ake zargi, gudanar da bincike, tabbatar da bin doka da kuma yaƙi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, kare rayuwar ɗan Adam dole ne ya kasance babban abin la’akari.
Kwamandan ya jaddada cewa nauyin kare al’umma da tabbatar da bin doka ya kamata ya kasance tare da kare mutunci, tsaro da walwalar mutanen da ke hannun jami’an tsaro.
A ƙarshe, Commandant Kabara ya roƙi Allah Ya gafarta wa waɗanda suka rasu kurakuransu, Ya ba su hutawa ta har abada, sannan Ya bai wa iyalansu, ‘yan uwa da masoyansu haƙuri da ƙarfin jure wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba.
Related Posts
Add A Comment
