Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, da mai bashi shawara kan harkokin siyasa Ibrahim Masari su jagoranci sanya ido kan yadda zaben fidda gwani na yan takarar majalisar tarayya da sanatoci na jamiyyar APC zai gudana.
Daga cikin aikin da tawagar masu sanya idon zasu yi a zaben fidda gwanin ya hadar da taba alli da gwamnonin jihohi na APC, da kuma kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa, da shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai da sauransu domin samun damar sauke nauyin da shugaban kasar ya dora musu cikin nasara.
Za kuma su tattauna da gwamnonin da shugabannin jam’iyyar na jihohi don samun maslaha wajen gudanar da zaben fidda gwanin cikin nasara.
