Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya musanta jita-jitar da ke yawo cewa akwai sabani tsakanin sa da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya na mai cewa dangantakar su na nan cike da amincewa da haɗin kai.
Abbas ya bayyana hakan ne a Zariya yayin rabon buhunan taki 60,000 ga manoma ƙarƙashin shirin Renewed Hope Fertiliser Distribution 2026.
Ya buƙaci mambobin jam’iyyar APC da su kasance masu haɗin kai da biyayya ga dokokin jam’iyya, tare da gujewa yaɗa jita-jita da kalaman da za su iya haddasa rarrabuwar kai.
A cewarsa, bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya fi muradun jam’iyya da ci gaban al’umma muhimmanci ba.
Abbas ya ce babu wani lokaci da gwamnatin Jihar Kaduna da ‘yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa daga jihar suka samu kyakkyawan haɗin kai kamar yadda ake da shi a yanzu.
Ya ƙara da cewa shi da Gwamna Uba Sani su na aiki tare bisa amana, girmama juna da kuma burin inganta rayuwar al’ummar jihar.
Kakakin Majalisar ya jaddada cewa masu ƙoƙarin haddasa saɓani tsakaninsa da gwamnan ba za su yi nasara ba, domin haɗin gwiwarsu ya ta’allaka ne kan samar da ci gaba da gudanar da ayyukan alheri ga al’ummar Kaduna.
Haka kuma, ya buƙaci mambobin APC su gudanar da harkokinsu na siyasa cikin natsuwa, su kauce wa ƙiyayya da son zuciya, tare da fifita haɗin kan jam’iyya da ci gaban jihar.
Abaya dai wasu sunyi hasashen shugaban majalisar wakilan yana kwadayin kujerar Gwamnan jihar ta Kaduna.
