Hon Alhassan Ado Doguwa ya bayyana gudunmawar da malamai suke bayarwa a fannin koyo da koyarwa da cewar Babban Al,amari ne da baza,a iya biyan su ba,sai dai Allah bisa yadda suke kashe lokacinsu domin bada ilimi.
Hon Alhassan Ado Doguwa ya na wannan bayaninne alokacin da ya halarci taron bada kyaututtuka na daliban makarantar federal government college kano Wanda aka gudanar a harabar makarantar dake unguwa uku.
Doguwa ya ja hankalin dalibai da su maida kai wajen karatuttukansu suyi ladabi da Da,a ga malamansu.

Doguwa ya ce ko wanne lokaci kofarsa a bude take muddin dai makarantar ta federal government college kano tana da bukatar taimakonsa yace ba iya shi kadai ba har zuwa shugaban majalisar kasa RT HON TAJUDDEEN ABBA’S,zai wuce gaba yayi musu iso idan da bukatar hakan.
… Hon Alhassan Ado Doguwa ya bada kyautar naira dubu dari ga Daliban da sukayi kwazo a fannin Al,adun gargajiya.
Kana ya kaddamar da littattafai da makarantar ta yi,kana ya sayi guda 2 akan kudi naira dubu dari 5,kana ya sadaukar dashi ga kananan hukumomin Tudun wada da Doguwa.
Shugabar makarantar ta federal government college kano Mrs Hafsah Adebayo ta yabawa RT HON ALHASSAN ADO DOGUWA bisa amsa gayyata da kuma Tallafin da yake baiwa makarantar
