Anbukaci Al, ummar jihar kano da su baiwa tsafta mahimmanci tare da tsaftace magudanan ruwa.
Tsohon shugaban karamar hukumar Tarauni kuma mashawarcin gwamnan jihar kano a kan harkokin yada labarai Hon Ahmad Aruwa shine yayi wannan kiran alokacin da yake bada umarnin gyaran magudanan ruwa dake yankin kundila Maiduguri road da kewaye.
Hon Aruwa yace wannan na cikin kudurin gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf,na gudanar da tsaftar muhalli mai taken TSAFTA GIDA-GIDA,domin kaucewa yaduwar sauro da sauran kwari masu cutarwa.

Aruwa yace tsaftace muhalli yana da asali da tasiri ko da a musuluncine domin Addini yayi kira da ayi tsafta.
Hon Ahmad Aruwa ya kashe makudan kudade ya yin gyaran magudanan ruwa a yankin karamar hukumar Tarauni domin samar da yanayi mai kyau.
yayinda Al, ummar yankin ta bakin malam isah mai Dala,ilu suka godewa Hon Ahmad Aruwa bisa wannan gagarumin aikin tsaftar muhalli da yayi ya kara da cewar,abune da ba,ataba yin irinsa a yankin ba.
