Cutar Diphtheria Ta Hallaka Yara Sama da 50 a Kano
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta ɗaukar matakin gaggawa domin shawo kan barkewar cutar Diphtheria da aka ruwaito a Ƙaramar Hukumar Rano, wadda ‘yan majalisar suka ce ta yi sanadin mutuwar yara sama da 50.
Kiran ya biyo bayan wata muhimmiyar sanarwa ta gaggawa da ɗan majalisar mai wakiltar mazabar Rano, Ibrahim Muhammad, ya gabatar yayin zaman majalisar, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Jibril Ismail Falgore.
Ɗan majalisar ya bayyana cewa cutar ta fi tsananta musamman a ƙauyukan Ridin da Sabuwar Ƙaura, inda aka ruwaito cewa yara sama da 50 suka rasa rayukansu sakamakon barkewar cutar.
Ya ce duk da cewa an fara ɗaukar wasu matakan gaggawa, ciki har da samar da magunguna da tura jami’an lafiya zuwa yankunan da abin ya shafa, har yanzu ana buƙatar ƙarin tallafi cikin gaggawa domin dakile yaduwar cutar.
Related Posts
Add A Comment
